Friday, 5 January 2018

Salah da Asisat Oshoala sun zama gwarzayen CAF na 2017

Dan wasan gaba na Liverpool da Masar Mohamed Salah ya zama gwarzon dan kwallon kafa na hukumar kwallon kafa ta Afirka, CAF na shekara ta 2017. Dan wasan mai shekara 25, wanda ya ci kwallo 17 a gasar Premier ta bana, ya taimaka wa kasarsa Masar ta samu gurbin gasar cin kofin duniya da kuma zuwa wasan karshe na gasar cin kofin Afirka a 2017.


Salah, wanda shi ne daman ya zama gwarzon dan kwallon Afirka na shekara na BBC a watan Disamba, ya doke abokin wasansa ne a kungiyar Liverpool Sadio Mane a gasar ta CAF.

Dan wasan gaba na kungiyar Borussia Dortmund da Gabon Pierre-Emerick Aubameyang shi ne ya zo na uku.

A bangaren mata 'yar wasan Najeriya da kuma kungiyar mata ta Arsenal Asisat Oshoala ita ce ta ci kyautar ta gwarzuwar 'yar kwallon kafa ta nahiyar ta Afirka ta shekara ta hukumar ta CAF.

'Yar kwallon mai shekara 22, da ta ci kyautar a karo na biyu wadda ke cike da shaukin wannan nasara ta shawarci matasan 'yan kwallo mata da su yi koyi da irinta kamar yadda ta cimma burinta.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment