Wednesday, 10 January 2018

"Shekaru 8 na kwashe ina aikin wankin gawa dan in samu biyan kudin makarantana">>Gwamnan jihar Oyo Ajimobi

Gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi ya bayyana cewa shekaru takwas yayi yana aikin wankin gawa a kasar waje domin ya samu kudin da zai rika biyawa kanshi kudin makaranta, gwamnan ya bayyana hakane a gurin wani taron matasan Yarbawa da akayi a jihar Osun inda ya halarta.Yace, a shekarar 1963 ya tafi kasar waje dan yin karatun boko kuma tunda ya fara karatun har ya gama dala talatin kawai aka aikamai daga gida, wannan yasa dole ya nemin aikin wankin gawa ya rika yi har tsawon shekara takwas daya kwashe yana karatu dan ya samu kudin biyan makaranta.

Ya kara da cewa lokuta da dama idan ya tashi daga aiki ya koma gida sai yayita kuka idan ya tuna gawarwakin da yake wankewa, amma sai maigidanshi yacemai ya daure dama da yawa idan suka fara aikin, irin wannan na faruwa dasu, amma ya rika kallon gawarwakin kamar sandararrun kifaye.

Gwamnan ya kara da cewa ya bayar da wannan labari nashine domin ya karfafawa matasa gwiwa, idan ka tsinci kanka a cikin wahala kada ka sare akan abinda kake nema, wata rana sai labari.
Kamar yanda jaridun punch da Vanguard suka ruwaito.

No comments:

Post a Comment