Tuesday, 16 January 2018

Shin da gaske Nafisa Abdullahi tasha Sigari: Me yasa take tallata hotunan shan sigarin nata?

Hotunan tauraruwar fina-finan hausa, Nafisa Abdullahi na shan taba sun dauki hankula soaai aka yi ta bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai, wasu na Allah wadai wasu na tunanin tasha tabarne da gaske, wasu kuma na yaba mata.


Nafisa Abdullahi Ta Sha Tabarne da gaske?

Amsar wannan tambaya itace, Eh! Nafisa tasha tabar a cikin wani shiri data shirya me suna Yaki A Soyayya, duk da cewa a cikin fim ne tasha tabar amma gaskiyane domin kuwa ta zuka hayaki ya fito irin na masu ahan taba.

Me yasa Nafisa take nuna wadannan hotuna?

Nafisa Abdullahi na nuna wadannan hotunane bisa dalilai guda biyu, na daya shine tallata wannan sabon fim nata da zai fito kasuwa, musamman masoyanta dama masu sha'awar fina-finan Hausa, ganin wadannan hotunan zaisa su kagu fim din ya fito kasuwa dan suka irin wainar da aka toya a ciki.

Abu na biyu da yasa Nafisar ta saka wadannan hotuna nata tana zukar taba sigari shine, jan magana, dama dai tun a farkon shekararnan Nafisar ta bayyana cewa ta shigo wannan shekarane da neman magana, kuma ta saka wadannan hotunan nata na shan tabane dan taga abinda mutane zasu fada akai.

No comments:

Post a Comment