Sunday, 7 January 2018

Shin wai Jam'i sukeyi ko Nafila: Me kuka fahimta?

Wannan hoton na gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ne da alamu ke nuna cewa kodai yana jan sallah ko kuma yanayin nafilane, hoton ya dauki hankula sosai inda akata muhawara da bayyana mabanbanta ra'ayoyi akai.Wasu dai sunce wai gwamnan ne kadai da mutumin bayanshi, mutum daya kamar yanda ake gani suke sallah, kuma wai ba'a hada kafada da gwamnane shiyasa duk da cewa su biyune kawai dole ya tsaya a bayan gwamnan suke jam'in a haka, wannan yasa wasu suka soki wannan yanayi na yin sallar.

Wasu kuma sunce wai, Nafilace su biyun sukeyi bawai jam'iba.

Yayinda wasu kuma sukace, tsabar sharrin makiyane ake surutu akan wannan hoton, domin kuwa idan ka kalli gaban hular mutumin bayan gwamnan da kyau, zaka fahimci cewa bashi kadai bane a bayan gwamnanba, mutum biyune, amma tsabar adawace tasa ake sukar hoton.

Wane ra'ayi kuka yadda dashi a cikin ukunnan?

No comments:

Post a Comment