Sunday, 28 January 2018

Shugaba Buhari tare da tsohon shugaban kasa, Obasanjo suna dariya a gurin taron AU

Shugaban kasa, muhammadu Buhari kenan a gurin taron kungiyar hadin kan kasashen Afrika a kasar Itofiya, Shugaba Buharin yana tare da tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo wanda ya aikamai da wasikar cewa kada ya tsaya takara a zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu.Wannan wasika ta jawo cece-kuce inda wasu suka ta tada jijiyar wuya suka yi zafafan kalamai, to yau ga shuwagabannin nan tare suna ta dariya, alamar cewa babu wani abu a tsakaninsu, dan gani kashenin siyasa ya kamata ka sake tunani.
Tare da shugaba Buharin akwai tsohon shugaban kasa, Abdulsalam Abubakar da ministan jiragen sama, Hadi Sirika dana Sharia dadai suransu, muna fatan Allah ya dawo dasu gida lafiya.
No comments:

Post a Comment