Tuesday, 23 January 2018

Shugaba Buhari ya amshi bakuncin shugaban kasar Equatorial Guinea

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amshi bakuncin shugaban kasar Equatorial Guinea, Obinag Nguema Mbasogo yau a fadarshi dake Abuja, a wata ganawa da sukayi da manema labarai, shugaban kasar Guinea din ya bayyana cewa yayi farin ciki da zuwa Najeriya da kuma ganin shugaba Buhari ya warware daga rashin lafiyar da yayi.Haka kuma ya kara da cewa ya jinjinawa shugaba Buharin kan namijin kokarin da yayi wajan yakar kungiyar Boko Haram dake addabar kasashe da dama da ayyukan ta'addanci, ya kara da cewa dolene shuwagabannin yankin su hada kai dan ganin an samar da tsaro me inganci, domin duk kasar da ta shiga matsalar tsaro to zai iya shafar makwauciyarta.
Haka kuma ya kara da cewa ta fannin samarwa al'umma abubuwan cigaba ma ya kamata shuwagabannin su hada kai dan ganin an samar da cigaba me dorewa.

Ya kuma ce kasarshi ta Equatorial Guinea na maraba da 'yan kasuwar Najeriya dan su shiga kasar shi dan yin kasuwanci.

No comments:

Post a Comment