Thursday, 4 January 2018

Shugaba Buhari ya bude tashar jiragen ruwa ta doron kasa a Kaduna: yace ana gina irin wadannan tashoshi a jihohi shida: ya koma Abuja

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kuma kaddamar da tashar jiragen ruwa ta doron kasa irinta ta farko a Najeriya, a Kaduna, a jawabinshi na gurin kaddamar da wannan tasha, shugaba Buhari yayi kira ga ma'aikata da kuma 'yan kasuwa dasu bayar da hadin kai wajan ganin wannan tasha tayi aiki yanda ya kamata.Shugaba Buhari ya kuma yanawa gwamnatin jihar Kaduna bisa irin gudummuwar data bayar wajan ganin wannan tasha ta kafu, yace wannan tasha zata saukakawa yan kasuwa masu shigo da kaya daga kasashen waje da masu fitar dasu yin kasuwancinsu cikin sauki, komi mutum zai iyayi anan ba sai yaje bakin ruwa ba.

Tashar an hadata da titi da titin jirgin kasa haddama ta jiragen sama duk za'a rika kawo kaya daga tashoahin jiragen ruwa dake gabar teku, hakan zai rage yawan kudin da ake kashewa wajan biyan kudin daukar kaya kuma zai habbaka kasuwanci da harkar tattalin arziki.

Shugaba Buhari yace akwai irin wannan tashoshi guda shida da yanzu haka ana kan gidansu, a Kano da Jos, da Aba, da Ibadan da Funtua da kuma Maiduguri, shugaba Buharin yayi kira da masu aikin gina wadannan tashoshi dasu hanzarta wajan ganin an kammalasu akan lokaci kumagwamnonin jihohin da ake gina wadannan tashoshi suyi koyi da gwamnan jihar Kaduna wajan bayar da duk irin guduwar data dace dan ganin aikin ya kammala.

Bayannan shugaba Buhari ya koma Abuja.

No comments:

Post a Comment