Saturday, 27 January 2018

Shugaba Buhari ya halarci taro akan zaman lafita da tsaro

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari kenan yau, Asabar a gurin taron samar da zaman lafiya da tsaro a kasashen Afrika daya gudana yau a Addis Ababa na kasar Itofiya, shuwagabannin Afrika sun tattauna batun rikice-rikicen dake faruwa a kasashe irinsu Libya, Somaliya, Afrika ta tsakiya da kuma rikicin Boko Haram.Ana saran shuwagabannin zasu fito da wasu tsare-tsare da zasu kawo karshen wadannan rikice-rikice dake faruwa. Wannan taron dai yana zuwane kwana daya kamin taron kungiyar hadin kan Afrika, AU da za'a gudanar gobe idan Allah ya kaimu.


Shugaba Buhari kenan yake gaisawa da sakataren majalisar dinkin Duniya, Antonio Guterres a gurin taron.
Shugaba Buhari kenan anan yake gaisawa da shugaban kasar Egypt, Abdulfatan Alsisi.

No comments:

Post a Comment