Saturday, 27 January 2018

Shugaba Buhari ya isa kasar Itofiya

A daren jiya, Juma'ane, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya isa Birnin Addis Ababa na kasar Itofiya inda zai halarci tarin gamayyar kungiyar hadin kasan kasashen Afrika da za'ayi acan.Shugaba Buharin ya samu rakiyar wasu daga cikin manyan jami'an gwamnati da suka hada da, Ministocin Shari'a dana harkokin cikin gida da shugaban hukumar yaki da yiwa arzikin kasa zagon kasa, EFCC dadai sauransu.


A wannan hoton na sama shugaba Buharine yake duba hotunan wadanda sukayi gwagwarmayar kafa kungiyar hadin kan Afrika.
Shugaba Buharine yake amsar filawar karramawa ta maraba da zuwa kasar Itofiyan.

No comments:

Post a Comment