Thursday, 4 January 2018

Shugaba Buhari ya kaddamar da sabbin taragwan jirgin kasa akan hanyar Kaduna zuwa Abuja: Yayi alkawarin karade dukkan manyan biranen Najeriya da jiragen kasa na zamani dan saukaka rayuwar Al'umma

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya kaddamar da sabbin taragwan jiragen kasa akan hanyar jirgin kasa daga Kaduna Zuwa Abuja,  Shugaba Buharin kuma zai kaddamar da tashar jiragen ruwa ta doron kasa wadda zata rika saukakawa 'yan kasuwar dake siyo kaya daga kasashen waje da kuma masu sayarwa zuwa kasashen waje, yanda zasu rika gudanar da komai anan Kaduna ba tare da sunje Legas ba.A jawabin da yayi a wajan bude taron, Shugaba Buhari ya kara tabbatar da ayyukan jiragen kasa da gwamnatinshi zatayi inda yace sai sun karade duk manyan biranen kasarnan da juragen kasa na zamani. 
Shugaba Buhari ya kuma ce suna kokarin kawo 'yan kasuwa masu zaman kansu dan su zuba jari a cikin harkar sufurin jiragen kasar, yace suna bukatar hadin kan masu ruwa da tsaki a wannan harka dan kawo cigaban zamani da saukaka rayuwar 'yan Najeriya.
A karshe shugaba Buhari ya godewa ministan sufuri, Rotimi Amaechi wajan kokqrin da yayi dan ganin wannan aiki ya kammala. Manyan mutane da jami'an gwamnati da suka halarci wannan furi sun hada da me masaukin baki, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da ministan sufuri, Rotimi Amaechi da shugaban 'yan sanda na kasa, Idris. Dadai sauransu.

No comments:

Post a Comment