Sunday, 28 January 2018

Shugaba Buhari ya yiwa Sanata Bashir Lado maraba da zuwa APC daga PDP

A jiyane rahotanni suka tabbatar da cewa sanata Bashir Garba Lado, tsohon me wakiltar Kano ta tsakiya a majalisar dattijai, wanda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kayar a zaben daya gabata, ya canja sheka daga PDP zuwa APC, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa da sanatan takardar maraba da zuwa APCn.A cikin wasikar daya aikemai, shugaba Buhari yace yayi farin cikin jin cewa Sanata Bashir din ya koma jam'iyyarsu a APC tare da dimbin masoyanshi kuma yaso ace ya sale samun damar zuwa Kano amma saboda irin yanda ayyuka suka mishi yawa, wanda yanzu haka yana kasar Itofiya halartar taron kungiyar hadin kan kasashen Afrika shiyasa.

Amma yana fatan haduwa da sanatan nan bada dadewa ba idan ya dawo.

No comments:

Post a Comment