Tuesday, 2 January 2018

Shugaba Buhari yayi Allah wadai da hare-haren jihohin Kaduna da Rivers

A wata sanarwa da shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya fitar ta hannun me magana da yawunsa, Mallam Garba Shehu, yayi Allah wadai da hare-haren da aka kai jihohin Rivers da Kaduna wanda sukayi sanadin rasa rayuka, ciki hadda wani basarake da me dakinshi dake dauke da juna biyu.Shugaban kasar ya jajantawa iyalan wanda wannan harin ya ritsa dasu, sannan yayi kira ga hukumomin tsaro da suke wadannan jihohi dasu kara akan kokarin da sukeyi na ganin sun kamo wadanda suka aikata wannan danyen aiki dan a hukuntasu.

Shugaba Buhari kuma yayi kira ga mazauna wadannan yankuna da kada suce zasu yi harin daukar fansa, su bari jami'an tsaro suyi aikinsu yanda ya kamata dan samun zaman lafiya me dorewa.


No comments:

Post a Comment