Monday, 1 January 2018

Shugaba Buhari zai Bude tashar jiragen ruwa ta doron kasa ta farko a Kaduna: Tashar zata samarwa mutane 300,000 aikinyi

Rahotanni sun bayyana cewa ranar Alhamis idan Allah ya kaimu, 4 ga watan Janairu na shekarar 2018 shugaban kasa Muhammadu Buhari zai ziyarci jihar Kaduna dan bude sabuwar tashar jirgin ruwa ta doron kasa da aka gina, irinta ta farko a Najeriya.


Jaridar Leadership ta bayyana cewa tashar wadda yanzu komai ya kammala da ake bukata ta fara aiki, idan aka budeta zata samarwa mutane dubu dari uku aiki na kaitsaye nan da shekaru biyar masu zuwa, hakanan kuma, a bayanin da jaridar ta tattaro ta bayyana cewa duk wani kaya da mutum zai siya daga kasar waje ko kuma zai sayar zuwa kowace kasa zai iya yin hakan a wannan tasha ta jihar Kaduna, ba sai yaje Legas ba.
Wani babban ma'aikaci a gurin ya shaidawa jaridar cewa bawai 'yan kasuwar Najeriya dake shigowa ko fitar da kaya daga kasashen waje kawai tashar zata amfanaba, harma da sauran irinsu dake kasashe makwauta, irin su Chadi, Kamaru, Nijar da Afrika ta tsakiya, sannan duk wani abu da mutum ke bukata na ya fitar da kaya ko kuma ya shigo dasu zuwa cikin kasarnan akwai tanajinshi anan Kaduna.

Itadai wannan tasha itace irinta ta farko a Najeriya, kuma musamman jama'ar Arewa zasu amfana da wannan tasha sosai fiye da kowa.

No comments:

Post a Comment