Thursday, 25 January 2018

Shugaba Buhari zai halarci taron kungiyar hadin kan kasashen Afrika a Itofiya gobe Juma'a

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kai ziyara Addis Ababa babban birnin kasar Itofiya, gobe Juma'a inda zai halarci taron kungiyar hadin kan Afrika da za'a gudanar, shuwagabannin kasashen Afrika da wakilansu zasu tattauna batutuwan da suka shafi yaki da cin hanci da rashawa da matsalolin tsaro da na hadin kai dana sauran muhimman batutuwa da suka shafi kasashen Afrika a taron.Bayan halartar taron, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari zai kuma yi ganawa da wasu daga cikin shuwagabannin kasashen Afrika da zasu zo taron.

Muna fatan Allah ya kaishi lafiya yasa ayi lafiya ya dawo dashi lafiya.

No comments:

Post a Comment