Thursday, 11 January 2018

Shugaban kasar Sudan, Umar Al-Bashir ya karrama Muhammad Indimi da digirin Dacta na girmamawa

A yau, Alhamis ne hamshakin attajirin dan kasuwa, Muhammad Indimi ya samu digirin Dacta ta karramawa da shugaban kasar Sudan, Umar Al-Bashir ya bashi daga jami'ar kasar sudandin ta kasa da kasa.


Sarkin Kano, Muhammad Sanusi na II ya shaida wannan karramawa da akawa Muhammad Indimi, A kwanakin bayane dai Muhammad Indimin ya bayyana cewa tunda yake bai taba shiga aji da sunan karatun boko ba.

Danshi, Ahmad Indimi ya tayashi murna a dandalinshi na sada zumunta.

No comments:

Post a Comment