Tuesday, 2 January 2018

Shuwagabannin Darikar kadiriyya sun kaiwa shugaba Buhari ziyara a fadarshi

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya amsi bakuncin 'yan Darikar Kadiriyya na nahiyar Afrika yau, Talata a fadarshi dake Abuja, bayan ganawar da sukayi, shugabannin Kadiriyyar, karkashin jagorancin, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara, sun mikawa shugaban kasar wata kyauta ta musamman da suka shiryamai.A cikin malaman da suka kaiwa shugaban kasar ziyara akwai, Sheikh Muhammad Hassan Fatahi, da kuma farfesa Hassan Abbas Hassan.

No comments:

Post a Comment