Thursday, 4 January 2018

Sojoji sun sake gano wata daga cikin 'yan mata Chibok dan Boko Haram suka sace

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun sake gano daya daga cikin 'yan matan Chibok da mayakan Boko Haram suka sace a shekarar 2014. Manjo Janar Rogers Ibeh Nicholas, kwamandan rundunar samar da zaman lafiya ta Operation Lafiya Dole, ya tabbatarwa BBC cewa an gano yarinyar ne ranar Alhamis da safe.


Wata sanarwa da mataimakin daraktan hulda da manema labara na rundunar Kanal Onyema Nwachukwu ya fitar ta ce an gano yarinyar ne a garin Pulka da ke jihar Borno.

A cewar sanarwar, "Zuwa yanzu, kwarya-kwaryar binciken da aka yi ya nuna cewa yarinyar, mai suna Salomi Pagu ita ce ta 86 cikin jerin 'yan matan Chibok da aka sace wadanda aka wallafa sunayensu a shafin intanet".
bbchausa

No comments:

Post a Comment