Monday, 29 January 2018

"Tabbas mune(APC sama da kasa) zamu sake cin zaben 2019">>Gwamna El-Rufai

A wani jawabi da yayi ta dandalinshi na sada zumunta da muhawara, Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa babu shakka sune(APC sama da kasa) zasu sake lashe zaben shekarar 2019 idan Allah ya kaimu.Gwamnan ya bayyana hakane a matsayin martani ga wasikar da tsohon shugaban kasa, Obasanjo ya aikewa shugaban kasa, Muhammadu Buhari akan cewa kada ya sake tsayawa takara a zaben shekarar 2019.

Gwamnan yace ya ga wasikar da Obasanjon ya aikewa Buhari amma saboda yawanta kuma ayyuka sun mishi yawa, be samu lokaci ya karantata ba, amma abinda ya sani shine tabbas sune zasu sake cin zaben shugaban kasa dana gwamnoni 24, harma da kari a shekarar 2019, saboda a Najeriya mutane kala biyune, da masu kudi da talakawa, kuma talakawa sune zasu ci zaben 2019 Idan Allah ya yarda.

No comments:

Post a Comment