Monday, 1 January 2018

TAFARKIN TSIRA (KASHI NA DAYA)>>Malam Aminu Ibrahim Daurawa

HADISI NA DAYA 
MANZON ALLAH SAW YACE:
DUK ALUMMA TA ZASU SHIGA ALJANNAH SAI WANDA BAYA SO !
 SAI SAHABBAI SUKA CE, WAYE BAYA SO, ? 
 SAI ANNABI SAW YACE : WANDA YA BINI ZAI SHIGA ALJANNAH, WANDA KUWA YA SABA MINI,  BAYA SO. BUKHARI YA RUWAITO.
 ‎
 ‎HADISI NA BIYU 
MANZON ALLAH SAW YACE, :
 ALUMMA TA  ZATA RARRABU GIDA SABAIN DA BAKWAI,  DUK SUNA WUTA SAI GUDA DAYA ! 
SAI SAHABBAI SUKA CE WACECE GUDA DAYAR ? 
SAI YACE ITACE JAMAA,  WADANDA SUKE KAN IRIN ABINDA NAKE KAI DANI DA SAHABBAI NA. ATTIRMIZIY YA RUWAITO.


 HADISI NA UKU ‎
MANZONALLAH SAW YACE, :
NA BAR MUKU ABU BIYU BAZA KU BATA BA MUTUKAR KUNYI RIKO  DA SU. 
1 LITTAFIN ALLAH SWT .
2 SUNNAR ANNABI SAW. 

HADISI NA HUDU 
MANZON ALLAH SAW YACE,: 
MAI RIKO DA SUNNA TA LOKACIN DA ALUMMA TA SAMU SABANI KAMAR MAI RIKO NE DA GARWASHIN WUTA. 

HADISI NA BIYAR
MANZON ALLAH SAW YACE:
KU RIKE SUNNATA DA SUNNAR KHALIFOFI NA
SHIRYAYYU.
HADISI NA SHIDA 
MANZON ALLAH SAW YACE: ADDINI NASIHANE, SAI SAHABBAI SUKA CE GA WAYE?  SAI YACE 
1 GA ALLAH SWT,
2 DA LITTAFINSA  
3 DA MANZONSA 
4 DA SHUWAGABANNIN MUSULMI. 
5 DA KOWA DA KOWA.  
MUSLUM,.
HADISI NA BAKWAI 
MANZON ALLAH SAW YACE: 
YANA DAGA CIKIN ALAMOMIN TASHIN ALKIYAMA ZAA DAUKE ILMI,  JAHILCI ZAI BAYYANA, 
ZINA ZATA YADU,  ZAA SHA GIYA,  MAZA ZASUYI KADAN MATA ZASUYI YAWA, HAR A WAYI GARI, MATA HAMSIN NAMIJI DAYA KE KULA DA SU. BUKHARI YA RUWAITO. 
HADISI NA TAKWAS 
MANZON ALLAH SAW YACE :  ALLAH BAYA KWACE  ILMI DAGA WADANDA SUKA SANSHI , SAI DAI YANA  KARBE ILMI TA HANYAR DAUKE MALAMAI,  HAR SAI AN WAYI GARI BABU MALAMAI,  SAI MUTANE SU RIKE JAHILAI A MATSAYIN MALAMAI,  SUNA YI MUSU FATAWA , SUNA BASU AMSA DA JAHILCI SAI SU BATA KUMA SU BATAR (DA ALUMMA).
KOWA YA AUNA AKIDARSA, DA IBADARSA, DA HALAYENSA DA MUAMALARSA . HAKA MANZON ALLAH SAW ,YAYI SHI DA SAHABBANSA.?
ALLAH KA AKAN SUNNAR ANNABI SAW, DA KHALIFOFINSA.

No comments:

Post a Comment