Saturday, 6 January 2018

Tsohon Mai Baiwa Gwamnan Taraba Shawara Ya Musulunta


...musulunci shine addinin gaskiya, cewarsa
Tsohon mai baiwa gwamnan Taraba shawara kan harkokin siyasa, Mista Adamu Kwanci ya karbi musulunci.Mista Kwanci ya ce bai yanke shawarar shiga addinin Musulunci ba sai da ya gudanar da bincike da dogon nazari, sannan karshen lamari ya gane cewar Musulunci shine Addinin gaskiya, sannan Musulmi sune jama'ar da su ka fi kowa son zama lafiya da tausayi. 

Mista Adamu Kwanci wanda a yanzu ya sauya suna zuwa Malam Adamu Muhammad Kwanci ya karbi kalmar shahada ne daga wajen Babban Malamin Addinin Musulunci nan mazaunin garin Jalingo Dakta Ibrahim Jalo Jalingo. Sannan ya yi alkawarin zama jakadan Musulmi wajen wayar wa Kiristocin Jihar Taraba kai akan gaskiyar Musulunci da Musulmi, su gane karya da sharri da ake yi wa Musulmi a jihar da Nijeriya dama duniya baki daya.
Rariya

No comments:

Post a Comment