Monday, 29 January 2018

"Tsohuwar tauraruwar fim din Hausa, Rashida Mai Sa'a tayi aure a asirce"

Wani labari dake fitowa daga jarumin fim din Hausa, Salisu Fulani na cewa, tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, kuma me baiwa gwamnan jihar Kano shawara akan harkokin mata, Rashida Adam Mai'sa'a tayi aure.Salisu yace Rashidar tayi aurenne a asirce kuma daga ita sai 'yan uwanta da kuma na kusa da ita sosai ta gayyata hidimar bikin, tuni dai abokan aikin ta har sun fara tayata murna da fatan Alheri.

Muma muna tayata murna da fatan Allah ya bada zaman lafiya ya kuma kawo zuri'a ta gari.


No comments:

Post a Comment