Tuesday, 30 January 2018

Tsoro ne ya hana Kwankwaso zuwa Kano>>Gwamnatin Kano

Gwamnatin jihar Kano da ke arewacin Najeriya ta yi watsi da hanzarin da tsohon gwamnan jihar Injiniya Rabi`u Musa Kwankwaso ya gabatar, cewa magabata ne suka shawo kansa har ya janye aniyarsa ta ziyartar Kanon.


A ranar Talata ne aka tsara Kwankwaso zai kai ziyarar don halartar wani gangami, ziyarar da ta zo daidai da wani taron bangaren gwamnatin Jihar ta Dakta Abdullahi Umar Ganduje, wanda ba sa ga-maciji da juna, lamarin da ya jefa al`umma cikin fargabar barkewar yamutsi.
A hirarsa da BBC kwsamishinan watsa labaran jihar, Mallam Mohammed Garba ya sheda wa wakilinmu Ibrahim Isa cewa barazana ta fi yawa a cikin al`amarin Sanata Kwankwaso, don haka bai yi mamakin soke ziyarar tasa ba.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment