Tuesday, 16 January 2018

"Wai dana sha taba, bakinkune ko nawa?: Ni fa me nishadantarwace kuma koyan tarbiyya nike ta yaya zan koyawa wani tarbiyya?">>Nafisa Abdullahi

Irin yanda hotunan jarumar fina-finan Hausa, Nafisa Abdullahi na ahan taba suka rika daukar hankulan mutane, anin yayi kamari soaai, wasu sunyi kira a gareta da ta daina domin akwai maau koyi da ita.A cikin irin amsoshin data mayar akan irin wadancan kiraye-kiraye, Nafisar tace.

"Mutum bazai iya zukar sigari a cikin kwaciyar hankaliba?, kune kuka sha? Bakinku ne? Ku barni inji dadina kawai"
Nafisar ta kumace " Aiki nane ya bukaci hakan kuma nayi, nadan zuki sigari...a gaskiya sosaima na zuka, aiki kenan malam, idan mutane maau koyi dani sunga cewa hakan daidaine suyi, to wannan ba matsalata bace, nasune, zan sake maimaitawa, ba hakkina bane in kula da yanda suke gudanar da rayuwarau ba"
Haka shima wani daya cewa Nafisar" Masu koyar da tarboyya" ta mayar mishi da amsar cewa " Ta nan ka bullo kuma....ni me nishadantar da mutane ce, ta yaya zan koyawa wasu tarbiyya, bayan nima ina kan koyane?..idan har aka samu dacewa na koyar da wani abu a kokarina na nishadantar da mutane, to wannan abune me kyau, amma ba aikina bane koya dan kowa tarbiyyaba"

No comments:

Post a Comment