Sunday, 7 January 2018

Wani Babban Soja Wanda Ya Yi Fice A Yaki Da Boko Haram, Major Hassan Ya Rasa Ransa

Major Hassan Jajirtaccen Soja ne, kuma haziki wajen yakar Boko Haram a jihar Borno musamman a yankin Damboa, ya hadu da ajalinsa a lokacin da suke bata kashi da mayakan Boko Haram a dajin Bita dake kusa da karamar hukumar Damboa na Jihar Borno a ranar Jumma'a da ta gabata.


Mutuwar wannan namijin Soja ya girgiza al'ummar Damboa matuka.

Allah ka jikansa sa Rahama, ka sa Aljannar Firdausi ce makomarsa.

Rashin Major Hassan babban rashi ne kuma koma baya ne ga yakin da ake da Boko Haram.
Rariya

No comments:

Post a Comment