Saturday, 6 January 2018

Wani Dattijo Ya Ja Kunnen Wata Budurwa Kan Tura Masa Sakon Soyayya A Facebook

Wani dattijo mai suna Awwal Ibn Suleman ya nuna dattako inda ya gargadi wata budurwa wadda ke tura masa sakon soyayya a cikin akwatin sakonnin shafinsa na Facebook.


Dattijon wanda ya sanya ainihin hotonsa a shafinsa na facebook ya rubuta mata sakon cewa "  abokiyata wannan ainihin hotona kenan kuma ni ba dattijo ne ba saurayi ba kamar yadda kike dauka, don haka ki daina turo mani sakonnin soyayya, mu ci gaba da kasancewa abokai. Ina fatan kin fahinta"

Shin in kai ne za ka iya yin haka a maimakon bin hanyar yaudara?
Rariya

No comments:

Post a Comment