Monday, 1 January 2018

Wani masallaci a kasar Amurka ya biyawa wani mutum diyyar makudan kudin da kotu ta yankemai hukuncin biya dalilin kalaman batancin daya rubuta a jikin masallacin

Wani mutum a kasar Amurka me suna Abraham Davis daya yiwa wani Masallaci barna a jiyar Arkansas kuma ya rubuta kalaman zagi da fenti a jikin masallacin ya samu sha tara ta arziki daga limamin masallacin.


Bayan wannan aiki na Davis ya aikata a shekarar 2016, ashe kyamarar masallacin ta dauki hotonshi yana wannan ta'asa, jami'an tsaro sun kamashi daga baya, kuma an gurfanar dashi a gaban kuliya aka yankemai hukuncin aikin sakai wanda ba biya, sanna kuma zai biya diyyar wasu makudan kudi, in kuwa ba hakaba, zai yi zaman shekaru shida a gidan kaso.

Ya biya iya tararda zai iya biya har kudinshi suka kare, nan nefa ido ya raina fata, domin sauran dala dubu daya da dari bakwai cikin kudin tarar, amma bashi dasu, dayake ya baiwa hukumar masallacin da ya yiwa wancan laifi hakuri, sai  Limamin masallacin me suna Louay Nassri ya dauko kudin da aka tara za'ayi gyaran masallacin dasu, ya biyawa Davis tarar da kotu ta yanke mishi.

Nassri yace idan mutum yayi laifi ya kuma gane laifinshi yazo ya nemi a yafe mishi to ya kamata a yafemishi ako inane kuwa, wannan shi yasa suka yafewa Davis laifin daya musu kuma har suka kara mai da kyautatawar biya mishi kudin diyya.

Ya kara da cewa Davis ya riga yayi aikin sakai wanda babu biya da kotu ta sakashi sannan kuma yanzu kudinshi sun kare, shiyasa suka taimakamishi, kuma sun gayamai suna mai fatan nan gaba ya samu rayuwa me kyaune shiyasa sukamai wannan shatara ta arziki.

Ya kara da cewa munyi tunanin abinda ya kamata muyi kenan shiyasa mukawa Davis haka, kuma da yasan mu wane irin mutanene da bai aikata abinda ya aikataba.

No comments:

Post a Comment