Wednesday, 3 January 2018

Wasu yankunan Najeriya na cikin duhu saboda matsalar wutar lantarki da aka samu jiha: Hukumar wutar ta fadi dalili

Ma'aikatar wuta, ayyuka da gidaje tayi bayani akan matsalar wutar lantarki da aka samu jiya, Talata a kasarnan, bayan da aka fara samun ingantacciyar wutar lantarki nadan wani lokaci, a jiyane wasu yankuna na kasarnan suka fuskanci matsalar wutar.Ma'aikatar tayi bayani a dandalinta na sada zumunta da muhawara na Twitter, inda tace dalilin wannan tangarda da aka samu shine, hukumar sarrafa iskar gas da kuma rarrabashi ta kasa ta bayar da rahoton tashin gobara a daya daga cikin bututunta dake Legas kuma da iskar gasne ake amfani wajan samar da wutar.

Wannan dalilin yasa dole aka tsayar da rarraba wutar har sai an shawo kan waccan matsalar tukuna, kuma hukumar wutar tayi kira ga'yan Najeriya cewa tana fatan zasu yi hakuri da ita har zuwa lokacin da komai zai koma daidai.

No comments:

Post a Comment