Saturday, 6 January 2018

"Waye Cristiano Ronaldo: Yakamata Hausawa suyi koyi da yan kudu wajan nuna kishin mawaka da 'yan fim dinsu">>Adam A. Zango

Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki Adam A. Zango yayi wani bayani a dandali shi na sada zumunta da muhawara akan rashin kishin Hausawa da basa nunawa 'yan fim da mawakansu, Adamun yace wani labari ne ya gani a yanar gizo akan wani hoton dan kwallo Cristiano Ronaldo da jarumar fim din Hausa Hadiza Gabon wanda mutane keta cece kuce akai.Yace" Shin wai ma wanene Cristiano Ronaldo?, da za'aita wani magana akanshi dan Hadiza Gabon ta fauki hoto dashi, ya kara da cewa, ya kamata dai Hausawa suyi koyi da kabilun kudancin kasarnan, irinsu Yarbawa da Inyamurai, su rika girmama Mawakansu da 'yan fim dinasu.

Adamun kuma yace, shi fa ya yanke shawarar duk wani abu dazaiyi zai yishine kawai, bazai kara tunanin cewa wai shi dan fim ne ba, be kamata yayi kazaba, a a abu kaza ya kamata yayi, yace yana da 'yanci kamar kowane dan Adam saboda haka zaiyi rayuwarshi yanda yakeso.

Damadai a wani sakon sabuwar shwkara daya fitat Adamun yace za'a rika jin duriyarshi sosai saboda yanzu ya canja.

No comments:

Post a Comment