Tuesday, 16 January 2018

'Yan sanda sun kama Aisha Buhari ta bogi

Aisha Buhari
Rundunar 'yan sandan Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya, sun ce sun kama wata mata da ke yin sojan-gona a mastayin mai dakin shugaban kasar Aisha Buhari.Wata sanarwa da kakakin rundunar DSP Anjuguri Manzah ya aikewa manema labarai ta ce an kama matar, mai shekara 37 'yar asalin jihar Filato ne a birnin.


Sanarwar ta ambato kwamishinan 'yan sandan Abuja Mr Sadiq Abubakar Bello na cewa "rundunar ta yi holen wata mata Aisha Muhammed Bello da ke damfarar mutane da suna matar shugaban kasa Aisha Muhammadu Buhari.
"Matar, mai 'ya'ya hudu daga jihar Filato na yin amfani da sunan mai dakin shugaban kasa domin neman kwangila da tallafin kudi daga mutane, musamman shugabannin hukumomi da ma'aikatun gwamnati."
Sanarwar ta kara da cewa jami'an 'yan sandan sun kama ta ne ranar 10 ga watan Janairu bayan sun samu rahotannin da ke cewa ta nemi taimakon kudi a wurin wani jami'in hukumar Fadama III Project.
"Bayan an kama ta ne sai aka gano wata wayar tarho mai dauke da layin da aka yi wa rijista da sunan Aisha Buhari, mai dakin shugaban Najeriya. Ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano sauran mutanen da ta damfara, sannan za a mika ta a gaban kotu da zarar an gama bincike", in ji sanarwar.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment