Wednesday, 10 January 2018

"Yan siyasa cutarku suke: a kowace jam'iyya suke duk kansu daya">>Inji ma'aikacin bbc, Nasidi Adamu Yahaya

Ma'aikacin bbchausa, Nasidi Adamu Yahaya yayi wani kira ga mutane, musamman matasa da su tashi suyi ilimi, su dena biyewa 'yan siyasa, suna sawa suna fada akansu, domin kamar yanda yace, a kowace jam'iyya suke duk kansu daya.A wani rubutu da yayi a dandalinshi na sada zumunta da muhawara, Nasidi yace:

"Sun cuce ku, sun sace kudinku, sun kai 'ya'yansu makarantun kasashen waje sun barku da jahilci. Amma kullum kuna cewa su zaku zaba. Yakamata ku sani wadannan mutanen dukkansu daya, a kowace jam'iyya suke".

Nasidi ya kara da cewa " kwanakin baya na hadu da wani gwamnan Najeriya a London tare da wani sanata. Jam'iyyarsu daban-daban amma suna ta dariya tare. Idan sun dawo gida kuma susa kuyi fada a kansu. Wallahi sun mayar da ku sha ka tafi. Ya kamata a lura da kyau. A je ayi karatu. A nemi nakai".


No comments:

Post a Comment