Monday, 1 January 2018

Yanda Yakubu Dogara ya tallafawa kananan 'yan kasuwa a jihar Bauchi

Kakakin majalisar Wakilai, Yakubu Dogara da matarshi, Gimbiya tare da tawagarshi, sunyi rangadin wasu kasuwanni jiya, Lahadi, a Jihar Bauchi, inda Dogara ya gana da wasu kananan 'yan kasuwa ya kuma tallafa musu da tsabar kudade dan su kara jari.



Kamar yanda ake iya gani a wadannan hotunan cikin kananan 'yan kasuwar da suka samu wannan tallafi sun hada da masu sayar da Rake/Kara da masu sayar da Kifi/Kihi da masu sayar da Lemun Zaki hada masu facin tayar mota.

Muna fatan Allah ya sakamai da Alheri.

No comments:

Post a Comment