Friday, 26 January 2018

'Yansanda sun shawarci Kwankwaso daya fasa zuwa Kano

Rundunar 'yan sandan jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ta shawarci tsohon gwamnan jihar Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso, da ya soke ziyarar da ya yi niyyar kai wa jihar a ranar talata 30 ga watan Janairu, saboda barazanar tashin hankalin da za a iya samu.


Kwamishinan 'yan sandan jihar Rabi'u Yusuf ne ya bayyana hakan a wajen wani taron manema labarai da aka yi a birnin Kanon ranar Juma'a.

Mista Yusuf ya ce ya zama wajibi a shawarci Sanata Kwankwaso ya soke ziyarar tasa, duk kuwa da cewa yana da cikakkiyar dama da 'yancin walwala a matsayinsa na dan asalin jihar.

Ya kara da cewa rahotanni sun nuna cewa akwai matukar tsoro a zukatan al'ummar jihar na irin tashin hankalin da za a iya samu.

Sai dai kawo yanzu Sanata Kwankwaso bai ce komai ba game da matakin rundunar 'yan sandan.
bbchausa.

No comments:

Post a Comment