Friday, 19 January 2018

Yayi mota da dusar kankara a kan titi dan ya tsokani jami'an tsaro

A lokacin da tsananin sanyi yasa dusar kankara ke zuba a sassa daban-daban na Duniya, yara da matasa na amfani da wannan damar wajan yin wasa da dusar kankarar suyi mutum mutumi ko kuma wasu abubuwa daban-daban da itaa, kamar dai yanda mu kuma anan a inda ake da yashi yara ke wasa dashi a hada gida da dai sauransu, su kuwa mahukunta suna dagewane wajan kawar da dusar kankarar musamman daga kan tituna da hanyoyi dan samawa jama'a saukin rayuwa.



A kasar Kanada wani mutum ya tsokani jami'an tsaro inda ya je tsakiyar titi ya hada mota da dusar kankara, sai ya koma gefe ya labe, aikiwa da yake laifine ajiye mota akan titi sai ga jami'an tsaro sun biyo hanyar.
A cikin hotunan nan za'a iya ganin jami'in dan sandar yana duba motar da akayi da dusar kankarar, sunsha ta gaskece, amma sai abin ya basu dariya har suka ajiye wa wanda yayi motar takarda cewa abinda yayi ya birgesu.

No comments:

Post a Comment