Friday, 5 January 2018

Za Mu Ci Gaba Da Yi Wa Buhari Addu'a Duk Da Cewa Wasu Ba Sa So A Yi Masa Addu'a, Cewar Sheik Sani Yahaya Jingir

Shugaban Kungiyar Izala Sheik Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa za su yi wa Buhari addu'a duk da cewa wasu ba sa so a yi masa addu'ar. Kuma Malamin ya ce Buhari nasa ne kuma shugabansa ne, kuma shi bai zabi Buhari dan ya bashi wani abin duniya ba, shi ya zabi Buhari ne da kuma umarni da ya yi akan a zabe shi saboda Buhari yana da gaskiya kuma yana da amana, kuma yana fada da cin hanci da rashawa.


A karshe Malamin wanda ya bayyana hakan a yayin hudubar da ya gudanar a masallacin Juma'a na 'Yan Taya dake garin Jos a yau, ya yi addu'a ga kasa da al'ummar kasar dama duniya gaba daya.
rariya.

No comments:

Post a Comment