Thursday, 18 January 2018

"Zai Yi Matukar Wahala Buhari Ya Sake Cin Zabe A 2019">>Sheik Gumi

Fitaccen malamin addinin Musuluncin nan mazauni Kaduna, Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ya bayyana cewa zai yi matukar wahala Shugaba Buhari ya sake cin zabe a 2019 saboda al'ummar Nijeriya za su juya masa baya inda ya jaddada cewa cin zabensa ya danganta ne ga wanda zai fafata da shi.


Sheik Gumi ya kara da cewa Buhari ya kasa cika alkawurran da ya daukarwa 'yan Nijeriya sannan kuma ya bar wasu na tafiyar da gwamnati tamkar ya zama Shugaban je-ka- na-yi- ka. Ya ce, Buhari ya kulla yarjejeniyar siyasa da mutanen Kudancin kasar nan wadanda suka taimaka masa ya ci zabe amma kuma an wayi gari suna ganin wasu sun yi babakere a gwamnatin.
Rariya

No comments:

Post a Comment