Wednesday, 7 February 2018

"Adam A. Zango ya sissirfawa Ali Nuhu zagi"

Bayan da Ali Nuhu ya fito ya bayyana cewa kada wani masoyinshi ya zagi wani abokin sana'arshi, dalilin tashintashinar dake faruwar a masana'antar ta fina-finan Hausa, wani bawan Allah ya zargi Alin da barin yaranshi saida suka gama yiwa mutane tatas sannan yake fitowa da wannan gargadi.To saidai wani ya mayar mishi da martanin cewa Adam A. Zango dama tuni yana kullace da Ali Nuhun, domin kuwa a kwanakin baya ya taba zazzaginshi. Munutin yace, abin ya farune lokacinda Adamun ya saka hotunanshi da matarshi a farkon shekararnan, wanda abin ya dauki hankula sosai, shi kuma sai yayi kira ga Adamun cewa ya daina yada irin wadannan hotunan, yayi koyi da Ali Nuhu wajan kare mutuncin iyalanshi.

Mutumin ya kara da cewa Adamun ya bishi ta sakon sirri ya zazzagi Ali Nuhun ya kuma gogeshi daga cikin mabiyanshi a shafin Instagram.

Ga abinda mutumin ya rubuta kamar haka:
Adam A. Zango dai a wani yunkuri da ya fito dashi da yace yana so ya kawo gayara a masana'antar fina-finan Hausa, ya bayyana cewa ba da Ali Nuhu yake yi ba.

No comments:

Post a Comment