Wednesday, 7 February 2018

"Ali Nuhune ke turo yaranshi suna zagina:Sabo da haka zan rika ramawa">>General BMB

Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello ya fito fili ya bayyana cewa abokin aikinshi, Ali Nuhu ne ke turo yaranshi suna zaginshi da cin mutuncinshi hadda taba Iyayenshi, Bello ya kara da cewa Alin siyasace kawai tasa ya fito ya gayawa Duniya cewa kada masoyanshi su zagi kowa amma a boye shine yake siyawa yaranshi data suna zuwa suna zagin.Bello dai yace duk wanda ya kara zaginshi cikin yaran Ali Nuhun zai saka zagin daya mai kuma ya mayar mishi da raddi daidai gwargwado. Ga abinda Bellon ya rubuta kamar haka:
"
Amincin ALLAH (s.w.t) su tabbaka a gareku mabiya ALLAH (s.w.t) da mabiyya turbar Annabi Muhammadu (s.w.t) Ina kara mika godiyata da dinbim masoyana, da malamaina, da shuwagabannina, da abokan sana'ata wadanda sukayita bani shawara kan cewa nayi hakuri na cire duk posts din danayi kuma na amince nayi hakan saboda masoyinka kadai kan iya gaya maka gakiya duk dacinta.

Ya kai mai karatu, idan zakamin adalci kasan ni ba mai girman kai bane kuma ni ba mai raina na kasa dani bane bare har takai ga na raina na sama dani, kuma idan zakamin adalci kasan ba akan @adam_a_zango kadai na taba shiga rigima ba, wallahi duk wanda naga anyimar ba daidai ba a mutanen Kannywood ina fitowa fili babu munafunci na kare masa hakkinsa, wallahi bama nan kadai duk wanda yayimin kyakkyawar sani yasan cewa ko a ina kuma ko a hanya duk makamin dake hannun jami'an tsaro idan naga anacin zarafin 'dan-Adam ko bansan shiba sai na tsaya na kwatar mishi hakkinshi saboda darajar da ALLAH (s.w.t) ya yiwa 'dan-Adam.


Kamar yadda kuka sani bani na fara abinnan ba, zagin cin mutunci aka dinga min har saida na gagara hakuri na fara mayar da martani, ba'a son raina ba sai don tura takai bango.
Ban zagi @realalinuhu ba, har sai da naga na mukarrabansa sun yi chaa akanmu da zagi zarafi har takai ga iyaye, kuma na tabbata duk wanda yasan darajar iyayenshi bazai yi shiru yayin da yaga wasu suna zagin iyayenshi saboda idan ka cire ALLAH (swt) da Annabi Muhammadu (saw) babu wani sama da iyaye.

Maganar anan itace, nayi shiru na cigaba da harkokina, amma har yanzu mukarraban Ali Nuhu basu daina zaginmu ba, wannan ya nuna cewa a shafinshi na Instagram ya umarce su da su daina amma a bayan fage ya cigaba da tunzura su. Ni dai nasan cewa babu yaron da zai bijirewa ubangidanshi, wato kenan shi yaki ya mayar da martani a shafinshi don jama'a suce shi mai hakurine mai son zaman lafiya, amma ya saya musu wayoyi yana tura musu data suna aiwatar da umarninshi. Ai duk mai hankali yasan divide and rule, mu ba yara bane shiyasa nace harshe yasan abinda hakori ke taunawa.

Kuyi hakuri domin Insha Allah duk yaron Ali Nuhu daya sake zaginmu zan dauko zagin nayi posting kowa ya shaida kafin nayi raddi ga mai turosu."

No comments:

Post a Comment