Monday, 26 February 2018

An gano inda 'yan Boko Haram suka kai 'yan matan Dapchi

A wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa, tace, ta samu labari daga wata majiya akan inda mayakan Boko Haram ke tsare da 'yan matan makarantar Dapchi su dari da goma da suka sace, haka kuma bangaren boko Haram da ya balle, karkashin Al-barnawi ne ke da alhakin sace yaran.


Majiyar ta jaridar DailyTrust wadda bata so a bayyana sunanta ta bayyana cewa 'yan boko haram sun raba yaran gida biyune inda bangare daya suka dauke su zuwa kasar jamhuriyar Nijar a wani gari da ake kira da Duro.

Dayan bangaren na 'yan matan kuwa suka ajiyesu a Garin Tumbun Gini a karamar hukumar Abadam dake jihar Borno. 

A wata ganawa da yayi da malaman jami'ar maiduguri uku da mata goma da boko haram din suka saki, Shugaba Bubari dai ya sha alwashin kwato dukkan matan da Boko Haram din ke rike da su.

No comments:

Post a Comment