Tuesday, 27 February 2018

An kai shugaba Buhari kotu saboda jan kafa wajan fitowa takarar shugaban kasa

Wata kungiyar matasa dake goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2019 sun kai shugaban kasar kara kotu saboda kin fitowa ya gayawa Duniya cewa zai tsaya takarar shugaban kasar.Kungiyar karkashin jagorancin dan majalisar jihar Nasarawa, Kassim Muhammad Kassim sun kai shugaba Buhari kotu ne saboda suna so ya fito ya amsa kiran miliyoyin 'yan Najeriya dake ta kira a gareshi da ya sake fitowa takarar.

Tun a ranar 15 ga watannan na Fabrairune kungiyar tayi wani gangami inda ta baiwa shugaba Buhari zuwa ranar litinin 19 ga wata da ya fito ya bayyana cewa zai tsaya takara ko kuma su kaishi kotu.


No comments:

Post a Comment