Wednesday, 7 February 2018

An sasanta tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango

Rahotanni dake fitowa daga masana'antar fina-finan Hausa na cewa an sasanta tsakanin manyan taurarin masana'antar biyu da rikici ya barke tsakanin mabiyansu, babban me bayar da umarni kuma jarumi, Falalu A. Dorayi ya bayyana wannan sasantawa da akayi tsakanin Ali Nuhu da Adam A. Zango.


Haka ma wani na hannun damar Adamun da ake kira da Malam Charki shima ya bayyana cewa an sasanta tsakanin Alin da Adamu. Muna fatan Allah ya kiyaye na gaba ya kuma karo zaman lafiya.

No comments:

Post a Comment