Saturday, 10 February 2018

An yankewa gawar soja hukuncin daurin kwanaki 40 a gidan kaso

Hukumar soji ta kasar Ghana ta yankewa gawar wani soja da ya samu hadari tare da wata mawakiyar kasar me suna Ebony Reigns kuma duka suka mutu hukuncin daurin kwanaki arba'in a dakin horo na gidan sojan.


Dalilin yankewa gawar wannan soja hukuncin shine, yayi karyar cewa bashi da lafiya yayin da zai fita daga barikin sojan kuma yaje gurin da ba hukumar sojance ta aikashiba da kakin soja, hukumar sojan tace ba zata bayar da gawarshi ga 'yan uwanshiba har sai gawar ta gama zaman hukuncin kwanaki arba'in din da aka yanke mata.

Haka kuma akwai yiyuwar cewa ba za'a baiwa iyalan sojan hakkokinshi na sojan da ya mutu ba saboda ba akan aiki ya mutuba kuma yayi karya.

Wannan hukunci dai ya dauki hankulan mutane da dama inda wasu ke ganin cewa yayi tsauri da yawa.
yen.com.gh

No comments:

Post a Comment