Wednesday, 14 February 2018

An yankewa likitan da yaci zarafin mata da kananan yara hukuncin shekaru 235 a gidan yari

Likita dan kasar Amurka da aka kama da laifin cin zarafin mata, kananan yara, an yankemai hukuncin zaman gidan yari na shekaru dari biyu da talatin da biyar, da farko dai manyan mata da kanana kimanin su dari biyu da sittin suka kai kararshi akan cin zarafin da ya musu lokacin da yake kula da lafiyarsu.Da farko dai an yankemai hukuncin shekaru dari da saba'in da biyar a gidan yari bayan daya amsa laifin cin zarafin kananan yara mata guda bakwai, sannan kuma zai yi zaman gidan yari na shekaru sittin a gidan yarin saboda samunshi da bidiyon batsa na kananan yara.


Andai tafi da Larry gidan bursuna a cikin jirgin sama na musamman, wanda hakan yasa wasu auka rika tambayar ta yaya mutum daya aikata irin wannan aika-aika za'a daukeshi a cikin jirgin sama na alfarma?

A cikin gidan bursunan dai za'a bashi riga me dauke da sunanshi kuma za'a bashi gado kuma zai iya yin amfani da kwamfuta amma banda shiga yanar gizo, saidai abinda ba'a bayyana ba shine ko za'a hadashi da sauran bursuna ko kuma za'a bashi dakime shi kadai.

Shine dai zai rika gyara dakinshi da shareshi.
Dailymail

No comments:

Post a Comment