Tuesday, 27 February 2018

An yi cushen gurbatattun malamai a cikin sunayen malaman makaranta da za'a dauka aiki a Kaduna

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yayi bayanin cewa an samu wasu bata gari sun cusa sunayen malamai da ba'a tantancesu ba a cikin sunayen sabbin malaman da za'a dauka aiki a jihar, dalilin haka yasa gwamnan ya sake bayar da umarnin sake tantance malam dan fitar da gurbatattu daga cikinsu.


Gwamnan yace idan suka kori gurbatattun malamai suka kuma maye su da wasu gurbatattun haka ba adalci bane.

Gadai jawabinshi kamar haka:

" Babu rashin adalcin da ya kai a ce mun kori gurbatattatun malamai sannan a ce wasu marasa kishi su cusa mana wasu gurbatattatun ta bayan fage. 

Mun sami Korafe korafen cewa an cusa sunayen wadanda ba su ci jarrabawar da muka yi ta daukan malamai Jihar Kaduna. Wannan dalili ne ya sa muka ce ba za mu yi kasa a gwiwa ba muka kafa kwamiti na musamman da za su tabbatar sun kara tantance wadannan sababbin malamai don tabbatar da an cire duk wadanda ba  su cancanta ba ko aka shigo da su ta bayan fage. Sannan mun roki su yi aikinsu tsakaninsu da Allah ba tare da la'akari da bambancin addini ko siyasa ba. 

Sannan duk wani jami'in gwamnatin da aka same shi da hannu cikin wannan danyen aiki da ake zargi, za a hukunta shi ta hanyar koran shi daga aiki ko kuma daukan mataki kamar yadda dokar aiki ya tanada. 

Ba zai taba yiwuwa mu sadaukar da duk wani burinmu na siyasa don ganin mun inganta rayuwar 'ya'yanmu amma wasu marasa kishi su zo su bata mana ba."

No comments:

Post a Comment