Thursday, 22 February 2018

Ana murna bako ya tafi...:Dambarwar masana'antar fim din Hausa ta dawo sabuwa

Ga dukkan alamu rikicin da ya so ya kunno kai a masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood da ake tunin an sasanta manyan jaruman, watau Ali Nuhu da Adam A. Zango na shirin dawo wa ko kuma ma ace ya dawo.


Domin kuwa Adamun ya bayyana cewa zai yi wata magana domin an kaishi bango, kamin yayi maganar ya cewa masoyanshi da abokai ya iyalanshi su gafarceshi, saidai be fito ya bayyana ko dawa zaiyi maganar ba kokuma akan me zai yi maganarba.
Adamun ya saka wannan hoton na sama me bayani akan abinda yake shirin yi.
Muna fatan Allah shi kyauta ya kiyaye fitina.

No comments:

Post a Comment