Monday, 5 February 2018

Anya Atiku zaikai labari kuwa?: Gwamnoni PDP sun zabi Sule Lamido a matsayin dan takararsu

Wani labari da shafin kwarmato na Sahara Reporters suka wallafa yace gwamnonin jam'iyyar PDP sunyi wani zama a jihar Delta inda suka yanke shawarar zabar tsohon gwamnan jihar Jigawa, Alhaji Sule Lamido a matsayin dan takararsu na shugaban kasa a zaben 2019 me zuwa.Sahara Reporters sun kara da cewa a labarin da suka samu gwamnonin sun zaunane akan tantancewa tsakanin Sule Lmidon da Tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar inda a karahe suka zabi Sule Lamido saboda irin gudummuwar daya bayar tun lokacin da aka kafa jam'iyyar ta PDP har zuwa yanzu.

Sunce Atiku be da kishin jam'iyya da burin kawo mata ci gaba, saboda ya cika tsallake-tsallake da yawa, daga wannan jam'iyya zuwa waccan.

No comments:

Post a Comment