Saturday, 24 February 2018

Anyi Allah wadai da Amina Amal akan irin hotunan da take sakawa: 'Bata so ana gaya mata gaskiyane'

A 'yan kwanakinnan jarumar fina-finan Hausa, Amina Amal ta rika saka hotuna  da mutane da yawa suka rika Allah wadai dasu wasu na gaya mata hakan  be dace ba dalilin haka yasa Amina ta kulle damar bayyana ra'ayi a ddandalinta na Instagram, watakila dan ba ta jin dadin irin maganganun da mutanen ke gaya mata. To saidai a yau Aminar ta saka wani bayani inda ta yabi kanta ta kuma bayar da damar a bayyana ra'ayi akai inda tace shin hakan gaskiyane?.Wannan hoton na sama me dauke da bayanin yabon da aminar ta wa kanta shine ta saka take tambayar cewa shin ko da gaske haka take, to saidai da alama wasu dama a hake suke suna jira, maimakon su bayyana ra'ayinsu akan wannan tambaya da tayi, sai suka rika gayamata rashin dacewar hotunan da take sakawa, inda sukayi Allah wadai da hana bayyana ra'ayi akan hotunan suka kuma zargi cewa bata so a gaya mata gaskiyane shiyasa tayi hakan.

Gadai kadan daga cikin irin abinda mutane suka gayawa Aminar.


No comments:

Post a Comment