Sunday, 4 February 2018

Aubameyanga yasha da kyar a hannun magoya bayan Arsenal bayan cin kwallonshi ta farko a wasansu da Everton: Ozil ya dauki hoto da Rihanna

Da alama kwalliya zata biya kudin sabulu ga kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a cefanen  da sukayi na siyo dan wasan gaba na kungiyar Dortmund, Aubameyang akan kudi Yuro miliyan 56, domin kuwa a wasansu da suka buga jiya, Asabar su da Everton wanda ya kare da ci 5-1, sabon dan wasan shima ya zura kwallonshi ta farko a mintuna 37 da fara wasan.
Dan wasan Arsenal, Ramsey yayi Hatrick, haka sabon dan wasan Arsenal din, Mkhitaryan ya samu yabo yayin da ya bayar da taimako akaci kwallaye 3, Laurent ne ya ciwa Arsenal kwallo ta biyar.

Ta bangaren Everton kuwa, dan wasansu, Dominic ne ya ci musu kwallon huce haushi kwaya tal.


Bayan kammala wasan, Aubameyang ya fito ya hau motarshi yayin da magoya bayan sabuwar kungiyar tashi ta Arsenal sukayi cincirindo a kanshi suna shewar murna da kiran sunanshi, da kyar ya samu ya fita daga cikin mutanen, kamar yanda wani hoton bidiyo ya nuna wanda Daily Mail ta kasar Ingila ta wallafa.
Haka kuma shahararriyar mawakiyar kasar Amurka, Rihanna taje kallon wannan wasa, bayan kammala wasan, ta taya yan wasan na Arsenal Murnar nasarar da suka samu har ta dauki hoto da Mesut Ozil. Ozil ya saka wannan hoton a dandalinshi na sada zumunta da muhawara inda yace"Sunyi nasara, kuma Rihana ma ta san kungiyar kwallon da ya kamata ta goyi baya".


No comments:

Post a Comment