Wednesday, 21 February 2018

(Aure nike so)'Allah ka ban miji na gari'>>Samira Ahmad

Kwanannan taurarin fina-finan Hausa mata dake fitowa fili suna nuna son yin aure na dada karuwa, a kwanakin bayane mukaji labarin Sa'adiya Kabala ta yi addu'ar cewa 'Allah ka aurad da mu' to Tsohuwar tauraruwar fina-finan Hausa, Samira Ahmad ma Ta yi shigen wannan addu'ar inda tayi rokon, Allah ya bata miji na gari.


Jarumar dai wadda tsohuwar matar tauraron fina-finan Hausace, T. Y Shaban ta yi wannan addu'ace a dandalinta na sada zumuna da muhawara, kuma jama'a da dama sun tayata da cewa Amin.

Muna muna mata fatan Allah ya amsa wannan addu'a tata.

No comments:

Post a Comment