Tuesday, 13 February 2018

"Ba zan zagi kowaba">>Cewar Abdul Mai Kwashewa bayan da aka ambaceshi a sakon da aka aikawa Nura M. Inuwa

Bayan da tauraron mawakin Hausa, Nura M. Inuwa ya bayyana sakon barazanar da aka aikamai na cin mutunci da cewa sai an sake illatashi, an ambaci sunan me bayar da umarni na fina-finan Hausa, Abdul mai kwashewa inda shima aka zageshi. Abdul dai yace su ba zasu zagi kowa ba domin ba irin tarbiyyar da aka musu ba kenan.


Saidai yayi fatan Allah ya bayyana me yin irin wannan abu.

Ga sakonshi kamar haka:

"Bambancin Mutum da dabba Hankali ....
Komai zakayi Kayi don Allah 
Idan zakayi Soyayya Kayi don Allah 
idan zakayi kiyayya kayi don Allah.
ALLAH YASA MU DACE.

To mudai bazamu zagi iyayen kowa ba kamar yadda kuka karewa iyayenmu zagi saboda ba ayimana tarbiyar hakanba a gida. 
Amma Allah ya bayyana kowaye sai mu dauras."

No comments:

Post a Comment