Monday, 12 February 2018

Bahaushe na farko: Me digiri na biyu: Ya bude gurin sayar da Abinci a kasar Ingila

Bahaushe na farko wanda aka bayyana sunanshi Abdullahi Mai Kano ya  bude gurin sayar da abinci a kasar Ingila, wanda ya bayar da labarin yace, baya ganin Hausawa a kasar Ingila suna neman kudi, ko kuma suna aiki a ma'aikatun kasar, ya kara da cewa yawancin Hausawan dake can karatu ne ke kaisu kuma da sun kammala suke dawowa Gida Najeriya basu cika tsayawaba.Haka kuma ya kara da cewa, duk kusan guraren sayar da abinci na bangaren da 'yan Najeriya sukafi yawa a kasar, 'yarbawa da inyamuraine suke dasu, amma gashi an samu bahaushe na farko daya bude gurin sayar da tsire, Kilishi da sauran kayan makwalashe.
Abdullahi ya sanyawa gurin suna, Alhaji Suya, kuma yana da digiri na biyu wanda ya samu a jami'ar Greenwich ta kasar Ingilar, labarin dai ya matukar kayatar da mutane sosai, muna mishi fatan Alheri.


No comments:

Post a Comment